Yajin Aikin Kungiyar ASUU Ya Kusa Zama Tarihi – Gwamnatin Tarayya

0
172

Gwamnatin tarayya ta ce kwanannan za’a shawo kan batun yajin aikin da kungiyar malaman jami’i’o ta ASUU ke yi.

Ministan kwadago da nagartar aiki, Dr. Chris Ngige ne ya bayyana hakan a jiya Talata yayin tattaunawa a shirin Politics Today na gidan Channels Television.

Ngige ya ce ma’aikatun kudi, Ilimi, Kwadago da Akanta Janar za su tattauna da kungiyar.

“Batun kungiyar ASUU zai zo karshe kwanan nan”, Inji shi.

Jawabin na Ngige na zuwa ne kwanaki uku bayan kungiyar ASUU ta ce ba za ta janye yajin aiki ba wanda ta fara a watan Maris.

Mataimakin shugaban kungiyar na ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce yajin aikin zai ci gaba har sai gwammatin tarayya ta biya bukatun kungiyar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here