
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga yan kasa gobe Alhamis, 1 ga watan Oktoba, da karfe 7 na safe a wani bangare na bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun yan cin ka.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a yau, ta ce Shugaba Buhari zai yi jawabi karfe 7 na safe sannan zai halarci wajen fareti a dandalin Eagle Sequare dake Abuja da karfe 10 na safe.