Mazauna Kano Sun Koka Bisa Yawaitar Sace-Sacen Garin Tuwo a Wajen Masu Nika

0
3883

Mazauna Unguwannin Kurna, Dandishe da Gobirawa dake Karamar hukumar Dala ta jihar Kano sun koka bisa yawaitar satar garin tuwo a wajen masu nika a jihar.

Jaridar PRIME TIME NEWS ta rawaito cewa mazauna unguwannin sun yi korafin yawan bacewar gari a wajen nika a yan kwanakin nan, wanda hakan ya haifar da damuwa tsakanin mutane, musamman ganin yadda tattalin arzikin kasarnan ke cikin mawuyacin hali.

Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa, masu karamin karfi ne wadanda baza su iya siyan shinkafa ba sai dai su ci abin da ya shafi gari musamman masara da gero, wanda dole ne a nika shi kafin a sarrafa shi.

Haka kuma, wannan jaridar ta gano cewa mazauna wasu yankuna a kwaryar birnin jihar Kano a yan kwanakin nan suna fuskantar yawan satar Gari a wajen masu nika, wanda hakan ya tilasta musu kula da abincin na su.

Mamman Sani, wanda ke yin nika a Gobirawa, Kurna ya bayyana cewa lamarin ya sanya shi cikin hatsari.

Ya ce, ya na yawan karbar korafin bacewar gari a shagon sa, wanda kuma dole ya biya, inda ya kara da cewa, ko a satin da ya gabata sai da ya biya dubu 15 na garin da ya bata.

“Ko satin da ya gabata, yan sintiri na vigilanta sun kirawo ni bisa matsalar batan gari, sai da na biya dubu 15, saboda garin akwai buhun da ya kai kilo gram 20, wasu kuma 15 wasu 10.

” A ko da yaushe ina maganin matsalar kuma da kudi na nake biya saboda dole ne na dauki hakan tunda shagona aka kawo garin”, inji shi.

Ya ce ya samar da shedar kati ga masu kawo nika, da lambobi wanda za’a gane masu garin kuma dole su nuna shi kafin su dau nikan su.

“Don kawo karshen rikicin da kokwanto, na yanke shawarar samar da katin sheda, mai dauke da lamba kuma dole ne kowanne mai nika ya nuna shedar da kudin nikan sa kafin ya dau garin sa”, inji shi.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya ce ya rasa buhun garin sa, lamarin da ya haifar da matsala a gidan sa.

” Na shiga damuwa sosai, saboda na siyi kwano 20 na masara bayan na karbi albashina na wata. Na yanke shawarar siyan gari da mai yawa wanda zai isheni amfani da shi har karshen wata. Sai dai cikin rasin sa’a, an sace shi.

“Amma, na karbi kaddarar Allah. Amma abun ba sauki”, Inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here