Gwamnatin Tarayya na shirin Siyar da Kamfanin Mai na Kasa NNPC

0
174

Gwamnatin tarayya na shirin sayar da kamfanin mai na kasa da kuma sake fasalin yadda ake raba kudaden da ake samu daga man fetur, kamar yadda sabuwar dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa Majalisar dokoki ta kun sa.

 

Daftarin dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa Majalisa, wadda ita ce ta farko tun bayan wanda aka fara aiki da ita a shekaru 20 da suka gabata, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito, na kunshe ne da yadda za’a sake dokokin da suka shafi hakar man da iskar gas sakamakon matsalar da ake samu wajen raba arzikin kasa.

Dokar ta kunshi bada damar kafa wani sabon kamfani wanda zai baiwa ministan kudi da na mai damar mayar da kadarorin kamfanin NNPC zuwa wurin, yayin da gwamnati zata biya hannayen jarin kamfanin wanda zai dinga gudanar da aikin sa a matsayin kamfanin kasuwanci wanda ba ruwan sa da kudaden hukuma.

Ana saran Majalisa ta kuma yi wa dokar man gyara dangane da abin da ya shafi yadda ake hako mai a cikin teku da kuma rage kudaden da kamfanonin hakar man ke baiwa gwamnati a wuraren da suke hako man da bai kai ganga 15,000 kowacce rana, daga kashi 10 zuwa kashi 7 da rabi ba.

Ana saran sabuwar dokar ta bada damar soke hukumar daidaita farashin man da kuma kirkiro sabuwar hukumar da za ta maye gurbin hukumar kayyade farashin man domin rage wasu ayyukan da hukumar DPR ke yi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here