Gwamnatin Jihar Katsina ta bada Umarnin Komawa Makarantu a Jihar

0
217

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da cewa za ta bude makarantu a jihar a ranar 5 ga watan Oktoba don cigaba da karatu.

Kwamishinan ilimi na jihar, Dr. Badamasi Lawal, ne ya bayyana hakan a yau Talata yayin zantawa da manema labarai a Katsina.

“Bisa shawarar gwamnatin tarayya ga jihohi na su duba yuwuwar bude makarantu don cigaba da karatu, mai girma gwammna, Aminu Masari ya amince da sake bude makarantun gwamnati da masu zaman kan su a jihar daga ranar 5 ga watan Oktoba”, inji shi.

Kwamishinan ya ce za’a yi amfani da makwanni uku wajen yin bitar karatu da yin jarrabawa yayin da zangon karatu na uku zai fara daga ranar 26 ga watan Oktoba wanda zai dau tsawon mako 15.

Ya ce don tabbatar da gudanar da ayyukan makaranta cikin kula da bin tsarin kariya daga cutar COVID-19, za’a dauki wasu matakan kariya kamar fadakar da masu ruwa da tsaki ta hanyar bada horo.

Dr. Lawal ya ce makarantu dole su tabbata cewa dukkan dalibai da ma’aikata sun sanya takunkumin rufe hanci da baki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here