Ayo Salami Ya Musanta Batun Cewa Ya yi Nadamar Shugabantar Kwamitin Binciken Magu

0
126

Ayo Salami, shugaban kwamitin fadar shugaban kasa dake bincikar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya ce baya nadamar kasancewa a kwamitin binciken.

Ana dai bincikar Magu ne bisa zargin tafikar da kudaden da aka kwato ba bisa ka’ida ba.

Sai dai lauyoyin Magu suna yawan kin amincewa da kwamitin binciken.

A wata takarda da aka fitar yau Talata, Salami ya soki lauyoyin bisa sanya rahoton cewa ya yi nadamar shugabantar kwamitin a kafafen yada labarai.

“Ba abinda zai sa na bayyana kowacce irin nadama bisa shugabantar kwamitin binciken, ina kallon nada ni da aka yi a matsayin shugaban kwamitin binciken a matsayin girmamawa.

“Ban taba nada wani daga cikin lauyoyin biyu ba wajen yin magana a madadina, zan iya bayyana abinda ke raina ba tare da bin hanyar lauyoyin wanda muke bincika ba”.

Sannan ya nemi yan Najeriya da suyi watsi da rahotan cewa ya yi nadamar shugabantar kwamitin inda ya ce ” Karya da bata suna” baza su hana kwamitin gudanar da aikin su ba.

Ya ce, Kwamitin wanda yake jagoranta zai ci gaba da binciken da yake yi kan Ibrahim Magu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here