An Samu Raguwar Masu Cutar HIV a Nijeriya -Rahotan Amurka

0
113

 

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa,  Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya ce ya miƙa rahoton ƙarshe na ƙididdigar ƙwararru kan alƙaluma da tasirin cuta mai karya garkuwar jiki na shekara ta 2018 a Nijeriya.

An gabatar da rahoton ne bayan bita da tantance sakamakon binciken.

Safiyon ƙididdige masu ƙwayar cutar HIVn, shi ne irinsa mafi girma da aka taɓa yi kan al’umma a faɗin duniya.

Sanarwar ta ambato jakadar Amurka a Nijeriya Mary Beth Leonard na taya murna ga Nijeriya saboda jagorancin da ta yi wajen aiwatar da ƙididdigar da kuma hanzarinta wajen amfani da sakamakon binciken don ya zame wa ƙoƙarinta jagora wajen shawo kan annobar HIV da AIDS tare da bunƙasa lafiya da walwalar al’ummarta.

Binciken dai a cewar sanarwar ofishin jakadancin Amurkan ya yi matuƙar inganta fahimtar da masu ruwa da tsaki ke da ita a kan cuta mai karya garkuwar jiki da kuma samar da muhimman alƙaluman da za su kai ga ɗaukar matakai, da ba da gudunmawar da ta dace da nufin samar da kula da lafiyar ceton-rai ga ‘yan Nijeriya fiye da miliyan ɗaya da ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki.

Jakadar ta kuma yaba wa Jami’ar Maryland, ta Baltimore a Amurka saboda matuƙar ƙoƙarinta wajen aiki da gwamnati da kuma sauran abokan ƙawance don gudanar da safiyon da kuma tsaida shawarar ƙarshe kan rahoton ƙwararru.

Sanarwar ta ce baya ga tallafin Global Fund a shekara ta 2018, gwamnatin Amurka ta hanyar shirin PEPFAR ta samar da tallafin dala miliyan 71 don gudanar da wannan ƙididdiga.

Safiyon dai in ji ta, ya samar da fayyataccen bayanan lafiya kan cuta mai karya garkuwar jiki da cutar hanta nau’in Hepatitis B da Hepatitis C a Nijeriya, da kuma ƙiyasta tasirin tallafin Shirin shugaban Amurka na gaggawa don yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki a tsawon shekara goma sha biyar.

A baya dai yawan masu fama da cutar ta HIV a Najeriya sun kai miliyan uku kuma Najeriya ce ta biyu a yawan masu fama da wannan cuta baya ga Afirka ta Kudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here