Za’a Saki Sakamakon Jarrabawar WAEC a Karshen Watan Oktoba

0
162

Hukumar dake shirya jarrabawar kammala Sakandire ta yammacin Afrika(WAEC) ta ce tana da kwanaki 45 daga ranar da aka kammala jarawabar karshe wajen sakin sakamakon jarrabawar na shekarar 2020. Wanda hakan ke nuni da cewa za’a saki sakamakon jarrabbawar a watan Oktoba.

An yi jarrabawar kammala Sakandire ta WAEC ne daga ranar 17 ga watan Agusta zuwa 12 ga watan Satumba, wanda hakan ke nufin cewa hukumar za ta saki sakamakon jarrabawar a ranar 27 ga watan Oktoba wanda yayi kwanaki 45 dai-dai da kammala zana jarrabawar.

Babban jami’in hulda da jama’a na hukumar shirya jarrabawar a Najeriya, Demianus Ojijeogu, ya ce “Kafin zuwan cutar Corona, muna sakin sakamakon jarrabawar kwanaki 45 bayan kammala zana ta, muna aiki don ganin mun yi hakan”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here