Bamu Ji dadin Yadda Dalibai Su ka Fadi Jarrabawar Qualifying Ba -Majalisar Dokokin Jihar Kano

0
165

Majalissar dokokin jihar Kano tace tayi takaicin faduwar dalibai jarrabawar qualifying dama tabarbarewar da ilimi a jihar nan yake yi.

Mataimakin kakakin majalissar dokokin jihar Kano kuma wakilin al’ummar karamar hukumar Makoda a zauren RT hon. Hamisu Ibrahim chidari shi ne ya bayyana haka yayin da ya jagiranci tawagar kwamitin duba musabbabin faduwar dalibai jarrabawar qualifying a jihar dama gano matsalolin da sauka addabi ilimin jihar zuwa wasu daga cikin makarantun sakandire na jihar Kano a yankin Kano ta arewa.

 

Itama anata bangaren shugabar makarantar Yan mata ta karamar hukumar Gezawa Hajiya Maryam Yusuf ta yabawa kokarin da majalissar dokokin jihar Kano ke yi na ganin halin da ilimi yake ciki kasancewa shi ne ginshikin kowacce al’umma harma ta zayyanawa kwamitin irin halin da makarantar take ciki.

 

Wakilin Jaridar PRIME TIME NEWS,  Sulaiman Auwal Marshall ya rawaito mana cewa tawagar Yan majalissar ta samun halartar kananan hukumomi da suka hadar da Bichi,Danbatta,Gabasawa da karamar hukumar ta Gezawa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here