
Mai Shari’a Shehu Atiku ya rasu yau a Kano bayan gajeriyar rashin lafiya.
Mai magana da yawun kotuna na jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar.
Sanarwar ta ce za’a binne gawar mamacin a gobe da misalin karfe 10:00 na safe.
Marigari Mai shari’a Shehu Atiku ya yi ritaya daga aiki a watan Janairu na shekarar 2015.