Yanzu-Yanzu: An Kara Kaiwa Gwamna Zulum Hari

0
168

An kara kaiwa tawagar Gwamman jihar Barno, Babagana Zulum, Hari a safiyar yau Lahadi.

Harin na baya-bayan nan ya faru ne a hanyar dawowar gwamnan zuwa Maiduguri.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an kai harin ne da misalin karfe 10:30 na safiyar yau a tazarar kilo mita 2 daga garin Baga.

Wasu daga cikin mutanen dake dawowa maiduguri a ranar Lahadi sun bayyana cewa ana zargin mayakan Boko Haram ne suka kai harin.

Wani daga cikin su ya ce”Ba’a samu asarar rai ba a lokacin sai dai wasu sun samu raunika.

“An fasa gilasan waasu motocin wasu kuma tayar su ta fashe sakamakon harin bindiga, ciki har da motar yan jaridun gidan gwamnati”.

A ranar juma’a ne dai aka kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari wanda yayi sanadiyar rasa rayukan mutane 30.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here