Yajin Aiki da Zanga-Zanga Na nan Daram a Gobe -NLC

0
159

Kungiyar Kwadago ta kasa(NLC), ta jaddada cewa za ta cigaba da shirin shiga yajin aikin da tsara yi gobe don kalubalantar karin kudin man fetir da na wutar Lantarki.

Kungiyar ta bayyana hakanne bayan tattaunawar sirri da kungiyar tayi da kakakin majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila.

Gbajabialmila ya tattauna da wakilan kungiyar ta NLC ne a yau Lahadi a harabar majalisar dake Abuja don shiga tsakani a turka turkar kungiyar Kwadagon da gwamnatin tarayya.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan tattaunawar, shugaban Kungiyar kwadago ta kasa, Ayuba Wabba ya ce kungiyar za ta shiga yajin aikin har sai gwamnatin tarayya ta kawo karshen lamarin.

Yayin da yake bayyana ra’ayin sa kan umarnin kotu na dakatar da kungiyar daga shiga yajin aiki, Wabba ya ce ba’a bawa kungiyar umarnin ba don haka bazai yi magana akan sa ba.

Haka kuma ya yi nuni da cewa akwai hukuncin kotu da ya dakatar da karin kudin wutar lantar ki amma gwamnatin tarayya taki ta yi biyayya ga hukuncin.

Shugaban NLC din ya ce abin da zai dakatar da su daga shiga yajin aikin shi ne gwamnati ta janye kudurin ta kafin 12 na rana.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here