Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanonin Mayakan Boko Haram

0
136

Rundunar Sojan Saman Najeriya ta Operation Lafiya Dole karkshin taimakon rundunar Operation Hail Storm 2 sun hallaka yan mayakan Boko Haram da dama a wani hari ta jirgin sama da suka kai mu su a sansanonin su dake Barno.

Jami’in Kula da kafafen Yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Asabar a Abuja.

Enenche ya ce nasarar da aka samu ta baya-bayan nan ita ce lalata sansanonin mayakan Boko Haram da dama a Tongule ranar 24 ga watan Satumba da wasu sansanonin dake Bone da Isari B Musa a ranar 25 ga watan Satumba.

Ya yi bayanin cewa luguden wuta da jirgin yakin saman sojan Najeriya ya yi a Garin Tongule ya zo ne bayan zagayen sirri wanda ya bankado cewa mayakan suna taruwa a yankin cikin dare.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here