Na yi Nadamar Kasancewa Shugaban Kwamitin Binciken Magu – Justice Salami

0
148

Mai shari’a Justice Ayo Salami ya ce ya yi nadamar shugabantar kwamitin bincike na fadar shugaban kasa wanda ke bincikar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, lauyoyi guda biyu da suke a wajen binciken ne suka bayyanawa jaridar PREMIUM TIMES hakan.

An yi zargin cwwa Salami ya yi bayanin hakanne a ranar juma’a yayin rufe sauraran jawabin kare kai daga Ibrahim Magu a fadar shugaban kasa dake Villa Abuja.

Kwamitin, wanda Justice Salami, tsohon shugaban kotun daukaka kara yake jagoranta, ya na bincikar zargin rashawa da zagon kasa biyo bayan korafin da antoni janar na kasa, Abubakar Malami ya yi kan Magu, wanda hakan ya kai ga dakatar da Ibrahim Magu daga shugabantar EFCC.

Zaman binciken dai ana gudanar da shi ne cikin sirri tare da hana yan jarida shiga zaman.

Sai dai yan Jarida suna samun bayanan da kwamitin ya tattauna ne daga bakin lauyoyi da kuma masu bada sheda da suka halarci wajen.

Kungiyoyin fararen hula sun nemi kwamitin binciken ya dinga zama a bayyane don tabbatar da anyi komai a bude da gaskiya.

Yayin da suke tattaunawa da Jaridar PREMIUM TIMES lauyoyin Ibrahim Magu wadanda suka halarci zaman kwamitin ranar juma’a, Tosin Ojaoma da Zainab Abiola, sun ce kafin fara zamam kwamitin, Mai shari’a Salami ya fada musu cewa ya yi nadamar karbar aikin jagorantar kwamitin binciken.

“Duk mun zauna a matsayin lauyoyi, bayan lokaci kalilan, Justice Salami ya ce ya yi nadamar yin aiki a wannan kwamitin binciken.

” ya yin da aka fara zaman jin bahasi, Salami ya na cike da yin nadama, ya dauko hankicin sa sannan ya ce yana matukar yin nadama da yin wannan aikin. Sai muka tambaye shi cewa , shin saboda ba’a samu shaida ko guda daya ba na zargin da akewa wanda muke karewa(Magu)?, Bai bada amsa ba sai dai ya ci gaba da cewa yayi nadamar yin aikin binciken”, iniji Misis Abiola.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here