Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Kama Samari da Yan Mata a Gidan Rawa

0
174

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama samari da yan mata 15,  bisa zargin aikata mummunar dabi’a a gidan rawa dake Kano.

Lawal Ibrahim, mai magana da yawun hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi a Kano.

Malam Ibrahim ya ce an kama samari da yan matan ne a ranar 20 ga watan satumba cikin tsakiyar dare a gidan rawar Al-Khairat dake Hotoro a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

“Acikin wadanda aka kama, 10 mata ne yayin da 5 maza ne masu shekaru tsakanin 18 da 22.

“Jami’an mu sun je wajen da misalin karfe 12:38 na dare tare da kama mutanen 15”, Inji shi.

Mai magana da yawun hukumar ya ce an tantance mutanen cikin tsanaki.

“Mun samu ce dukkan su wannan ne lokacin su na farko da aka kama su, mun kira iyayen su mun mika su gare su tare da gargadar su”, inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here