Dole ne Bankuna da Filayen Jiragen Sama Su Kasance a Rufe, Gobe -NLC

0
203

Kungiyar Kwadago ta ce dukkan bangarori ciki har da zirga-zirgar jiragen sama, Bankuna da sauran su za su kansance a rufe a yayin da ma’aikata za su yi zanga-zanga a gobe 28 ga watan Satumba.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Mista Amaechi Asogwuni ne ya bayyana hakan a taron manema labarai yau Lahadi a Birin Legas a yayin da ake shirin shiga yajin aiki.

“Babu wata tashar sauka da tashin jirgi da za ta yi aiki a Najeriya; Bankuna ma baza suyi aiki ba.

“Mu ma’aikata ne, baza mu je aiki ba; muna da yancin yin haka saboda zanga zanga hakkin mu ne da kundin tsarin mulkin kasa ya bamu.

“Kuma na yarda zamu tilasta hakan; makarantu za su kasance a kulle har sai an kawo karshen yajin aikin”, inji shi.

Asogwuni ya yi kira ga yan Najeriya da su shiga zanga-zangar.

” Zamu tabbatar da dukkan bangarori sun kansance a kulle don yin kira ga gwammati ta kula da kukan yan Najeriya”, Inji shi

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here