Masu Zaben Sarki a Masarautar Zazzau Sun Zabi Sabon Sarki

0
232

Masu Zaben Sarki da suka hada da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu , wanda shine shugaba, Makama Karami, Alhaji Muhammad Abbas, Fagacin Zazzau, Alhaji Umar Muhammad, Babban Limamin Zazzau, Sheikh Dalhatu Qasim da Babban Limamin Kona, Shekh Muhammadu.

Sun Zabi Iyan Zazzau, Bashir Aminu, wanda zai gaji tsohon sarkin Zazzau da ya rasu, Shehu Idris, wanda ya rasu ranar Lahadi yana da shekaru 84.

An yi zaben ne a gaban Sakataren gwamnatin jihar, shugaban ma’aikata, kwamishinan yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki.

Rahotanni sun bayyana cewa, uku daga cikin masu zabar sarki sun zabi Aminu Idris babban Dan Sarkin Zazzau da ya rasu yayin da Yariman zazzau da Munir Ja’afaru suka samu kuri’a daya kowannen su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here