Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi Na Taimakawa Boko Haram, Daba da ‘Yan Bindiga – Ganduje

0
170

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ayyana ta’ammali da miyagun kwayoyi a matsayin babban laifin da yake taimakawa Boko Haram, Daba, da rigimar kan hanya a kasarnan.

Ganduje ya yi kira a hada hannu da karfe wajen dakile lamarin.

Ganduje na fadin hakanne a yau Alhamis yayin kona jabun magunguna da hukumar hana sha da fatucin miyagun kwayoyi(NDLEA) ta kama a Kano.

Ganduje ya ce “Ta’ammali da miyagun kwayoyi shine babban laifin da ke taimakawa Boko Haram, Yan Bindiga, Yan Daba da fadace-Fadace akan hanya cikin al’ummar mu. Suna shan miyagun kwayoyi ne don aikata wadannan laifuka da sauran laifuka.

“Akwai bukatar a hada karfi da karfe wajen yin maganin matsalar tare da kawar da ita daga cikin al’ummar mu”.

Gwamman ya kuma yi bayanin cewa, gwamnatin jihar tana daukar matakai wajen ganin an dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi ta hanyar mayar da masu siyar da magunguna zuwa kasuwar zamani ta Kano dake Dangwauro.

Sannan kuma, dukkan hukumomin da abun ya shafa za’a samar mu su da ofisoshi a kasuwar don tabbatar da ba’a siyar da jabun magani ba a jihar.

“Dukkan masu siyar da magani da masu kawo magani za su koma kasuwar zamani nan bada jimawa ba dake Dangwauro”.

Ganduje ya bayyana cewa “shirye-shirye na kan hanya wajen samar da cikakken tsaro a sabuwar kasuwar da yan sanda, NDLEA, NAFDAC, NSCDC da sauran hukumomi don tabbatar da cewa ana siyar da magunguna masu kyau a Kano”.

Sannan ya ce dokar hana ta’ammali da miyagun kwayoyi za’a mika ta majalisa nan ba da jimawa ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here