Babban Hafsan Sojin Sama Ya Auri Ministan Jin Kai, Sadiya Umar Faruq

0
316

Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya auri ministan Jin kai da walwala, Hajiya Sadiya Faruq.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, an daura auren ne a ranar Juma’a, 18 ga watan Satumba, a masallacin juma’a na Maitama dake Abuja.

“Tabbas gaskiyane, babban hafsan sojin sama da ministan jin kai sun yi aure” cewar wata majiya.

“Mutane kalilan aka gayyata zuwa wajen daurin auren saboda Amarya da angon basa so su bayyana lamarin ga kowa”, inji shi.

Wata majiyar ta ce masoyan biyu sun jima suna soyayya.

” Sun dade suna soyayya, abin da ya faru ranar juma’a ya kawar da duk wani cece-kuce kan soyayyar ta da Buhari”, inji shi.

A watan Oktoba ne dai aka dinga yada jita jitar cewa ministan ta auri shugaba Buhari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here