Mun Shirya Lashe Zaben Shekarar 2023 -PDP

0
179

Shugaban kwamitin amintattu na jami’iyyar PDP, Sanata Walid Jibril, ya ce jami’iyyar na shirye-shiryen karkashin kasa don kara samun nasarar darewa mulkin kasa tare da samun nasara a kaso 90 a jihohin kasar nan, a zaben 2023.

Jami’iyyar PDP dai ta rasa mulki ne a zaben shekarar 2015, bayan shafe shekaru 16 ana mulkin.

Jibril, a cikin sakon kar ta kwana da ya aikawa wakilin jaridar Daily Trust a yau Laraba ya ce matukar hukumar zabe ta kasa INEC da gwammatin Buhari suka gudanar da zabe sahihin zabe, jami’iyyar PDP za ta samu nasara a zabsn tare da dawowa da martabar kasarnan.

Ya ce idan aka sake zaben jami’iyyar PDP, za ta kawo karshen matsalar tsaro a kasarnan.

“Bayan nasarar mu a zaben jihar Edo, PDP yanzu ta na mulkar jihohi 16 yayin da APC ke mulkar 19.

“Hakan na nuna alama mai kyau cewa PDP ta na kan hanyar samun nasara a kaso 90 na jihohin Najeriya idan INEC ta ci gaba da gudanar da sahihin zabe.

” Kofar mu kullum a bude take ga kowa ga dukkan mai son shiga jami’iyyar.

“Ya tabbata cewa ba wata jami’iyya da za ta mulki Najeriya cikin nasara sai PDP.

“Don haka dole ne yan Najeriya su bi hanya irin ta Edo kuma su kasance cikin shiri a zaben 2023”, . Inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here