Kwamishinan Karkara zai aurar da Zawarawa 50 a karamar hukumar Tsafe

0
130

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Kwamishinan raya karkara da birane na jihar Zamfara, Hon Abubakar Abdullahi Tsafe,zai aurar da Mata zawarawa hamisn da mazajan su dan ganin antallafawa mabuqatan yin auren da basu da halinyi.

Hon Abubakar Abdullahi Tsafe, ya bayyana haka ne a lokacin da ya amsa tanbayoyin ‘Yan jaridu a ofishinsa da ke Gusau.

Kwamishinan raya karkara ya bayyana cewa, ayau an wayi garin Zawarawa suna buqatar aure sunyi yawa kuma rashin kuxin hidimar ne ke kawo tsaiko.wannan ne ya sanya na ga ya dace ,da in sanya hannun jarina wajan xabaqa sunnar Mazan Allah (SWA) na samar da zuriya xayyiba.dan wasu na da Sana’ar da zasu iya riqe auren,amma kuxin auren ne ya gagara dan idan sun kwashe jalin nasu suka yi auren babu abun da zasuci bayan auren, amma idan aka taimaka masu da Sadakin suka kuma Mata Zawarawan da kayan xaki zai taimaka wajan xorewar auren.inji ‘Hon Abubakar Tsafe.

Kuma yanzu haka kwamitin tantance ma’auratan wanda ya haxa da likitoci,sun gama tantance su,waxanda suka da matsalar rashin lafiya irin ciwon Hanta da TV,an basu magunguna sun warke tas.yanzu lokacin muke jira daga gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun na ranar shagulgulan bikin.

Hon Abubakar Tsafe ya kuma bayyana cewa, “Umaba ga Zawarawan da su mazajan shine mai martaba “Yan dotan Tsafe, Alhaji Muhammad Bawa.kuma ta hannun Uban qasa goma sha bakwai da muke da su a faxin qaramar hukumar Tsafen ne aka samu waxannan Zawarawa da Mazajan auren na su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here