Kungiyar Masu Manyan Motoci ta Kasa Ta Dakatar da Yajin Aikin da ta Fara

0
159

Kungiyar masu manyan motoci ta kasa ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwana biyu wanda ta fara ranar Talata.

Ta dakatar da yajin aikin ne bayan shiga tsakani da kamfanin albarkatun man fetir na kasa NNPC da Hukumar tsaro ta farin kaya suka yi.

A ranar Litinin ne dai kungiyar ta NARTO ta umarci mambobin ta ciki har da masu dakon man fetir a fadin kasar nan su dakatar da gudanar da aiki bisa kin amincewa da matakin gwamnatin tarayya na hana motocin dake dakon mai da ya haura Lita 45, 000 hawa kan titunan Najeriya.

Sai dai shugaban kungiyar masu ababawan hawan ta kasa Yusif Othman, a jiya Talata ya bayyanawa yan Jaridu cewa uwar kungiyar ta tattauna da jami’an gwamnati don janye batun yajin aikin.

Kungiyar NARTO dai ita ce kungiyar masu ababawan hawa dake safarar kayayyaki, man fetir da fasinjoji a fadin kasarnan da yankin yammacin Afrika.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here