An Soke Auren Wata Budurwa a Jihar Sokoto Bayan Bayyanar Bidiyon Tsiraicin ta a Shafukan Sadarwa

0
331

Hukuma Hisbah a jihar Sokoto a jiya Talata ta ce ta kama mutane uku bisa yada Bidiyon Batsa wanda aciki daya daga cikin su yake lalata da tsohuwar budurwar sa.

Mutumin an zarge shi da yada bidiyon a shafukan sadarwa yayin da matar ke shirin yin aure a ranar 17 ga watan Oktoba.

Bidiyon ya nuna daya daga cikin wadanda aka kama yana lalata da matar yayin da abokin sa ke daukar Bidiyon.

Babban Kwamandan Hisba na jihar, Kasarawa, ya fadawa sashin Hausa na BBC cewa hukumar ta samu korafi ne daga mahaifiyar yarinyar.

Ya ce, Mahaifiyar yarinyar ta bada labarin cewa an dau Bidiyon ne a shekarar 2017.

Matar ta yi korafin cewa an sanya ranar 17 ga watan October a matsayin ranar Auren yar ta, sai dai yanzu an soke batun auren saboda angon ya fasa bayan Bidiyon Batsa na Amaryar ya bayyana a shafukan sadarwa.

Kasarawa ya ce: “Yaron ya yaudari yarinyar inda ya kai ta Hotel sannan ya dauki bidiyon tsiraicinta, yanzu bayan ta samu miji ta na shirin yin aure, sai kawai ya saki Bidiyom.

” Mun yi yaron tambayoyi, ya tabbatar da faruwar lamarin a hotel sannan mun kama abokan su guda biyu wadanda ya turawa Bidiyon. Kuma sun amince cewa an tura musu Bidiyon.

Hukumar ta ce za ta mika lamarin ga hukumar hana cin zarafin kananan yara da zarar ta kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here