Zaben Edo: Kawu Sumaila Ya yi Kira Ga APC Da Ta Hukunta Adam Oshiomole

0
135

Tsohon mai baiwa shugaban kasa Buhari shawara kan majalisar wakilai ta kasa, Abdulrahaman Kawu Sumaila ya yi kira ga uwar jami’iyyar APC ta kasa da ta hukunta tsohon shugaban jami’iyyar, Adams Oshiomole da dukkan wadanda suka jawo faduwar jami’iyyar.

Kawu Sumaila yana mayar da martani ne kan zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar ranar Asabar wanda Godwin Obaseki na jami’iyyar PDP ya kayar da Ize-Iyamu na APC.

Ya ce, ya kamata kwamitin riko na jami’iyyar APC ya yi duba na tsanaki kan rikicin jami’iyyar tun daga shekarar 2019 zuwa yau don hukunta masu hannu wajen lalata jami’iyyar.

Yayin da yake tattaunawa da manema labarai yau Talata a Kano, tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan ya ce duk da an gina APC kan tsarin sahihin zabe sai dai wasu wasu “rubabbu” sun ci amanar manufar jami’iyyar saboda son zuciyar su.

“Na yarda cewa wannane lokaci mafi dacewa da APC da za ta motsa da kuma hukunta duk wadanda suka haifarwa da jami’iyyar matsalar da take ciki, kuma hakan zai fara ne daga shekarar 2019 zuwa yau”, inji shi.

Sannan ya yi bayanin cewa jami’iyyar ta riga tayi magana kan zaben jihar Edo, inda ya kara da cewa ” duk wanda yake ganin matsayar jami’iyyar ba ta yi masa ba, zai iya daukar matakin shari’a da ya dace.

“Dauko Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ba komai bane illa rashin dai-dai, saboda a matakin farko gwamanan bashi da sani akan yadda aka kafa APC kuma bazai iya magana akanta ba”.

Kawu ya ce, Adam Oshiomole da yan koran sa sun kusa kai jami’iyyar rami ba dan tsayawar shugaba Buhari ba.

Sannan ya yi kira ga jami’iyyar da ta gaggauta yin bincike kan wadanda suka jawo faduwar ta don yi musu hukunci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here