Kungiyar Kwadago Ta ce Za ta Ci Gaba Da Shirin Gudanar da Zanga-Zanga Mako Mai Zuwa

0
108

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi ikirarin ci gaba da shirin ta na gudanar da zanga-zanga da kuma tafiya yajin aiki daga ranar 28 ga watan Satumba biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya na janye karin kudin man fetir da na wutar lantarki.

Shugaban kungiyar ta NLC, Ayuba Wabba, jim kadan bayan gudanar da taron kungiyar na kasa a Abuja yau Talata, ya ce mako mai zuwa kungiyar kwadagon za ta fara zanga-zanga da yajin aiki.

Ayuba Wabba ya yi bayanin cewa shugabannin kungiyar na jihohi 36 ne suka amince da daukar matakin

Idan za’a iya tunawa dai gwamnatin tarayya ta amimce da karin kudin wutar lantarki gami da na man fetir a ranar 1 ga watan Satumba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here