Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Ziyarci Buhari

0
222

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a yau Litinin ya karbi bakuncin shugaban kwamitin riko na jami’iyyar APC, Gwamna mai Mala Buni da gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Haka kuma Buhari ya tattauna da gwamnonin biyu ne cikin sirri sannan ba suyiwa yan Jarida bayanin abinda aka tattauna ba, sai dai ana zargin sun tattauna ne kan batun sakamakon zaben jihar Edo da aka gudanar a karshen Mako.

Dan takarar jami’iyyar APC, Ize-Iyamu ya sha kayi a hannun dan takarar PDP, Godwin Obaseki.

Ganduje wanda shine shugaban kwamitin yakin neman zabe na jami’iyyar APC ya shafe kwanaki a birnin Benin don ganin samun nasarar APC.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here