Osinbajo Ya Samu Jika

0
136

Daya daga cikin ya’yan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Damilola Osinbajo, da Mijin ta Bakare Seun Bakare sun haifi sabon jariri.

Osinbajo ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa, yar sa, Oludamilola da mijin ta Oluseun sun zama iyaye ga sabon jariri a safiyar ranar Litinin.

“Tsarki ya tabbata ga Ubangiji, yanzu na zama Kaka! Ya’ ta Oludamilola da mijin ta Oluseun sun zama iyaye a safiyar yau din nan”.

Itama mahaifiyar ta, Dolapo Osinbajo ta godewa Allah bisa samun jaririn.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here