Masari Ya Kaddamar da Sabbin Motocin Kungiyar Wakilan Kafafen Yada Labarai

0
183

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya kaddamar da sabbin motoci biyu da kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta NUJ Correspondents’ chapel ta samu

Masari ya kaddamar da motocin ne a gidan gwamnatin jihar a yau Litinin.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da motocin, Gwamnan ya yi kira ga shugabannin kungiyar wakilan kafafen yada labaran da su kula da motocin wanda zai sa su amfane su.

Masari ya yi nuni da cewa fannin sufuri ya na daga cikin fannonin cigaban tattalin arziki wajen samar da ayyuka ga dubban al’umma.

Tun a farkon jawabin sa, shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labaran, Abdulhamid Sabo ya ce kungiyar ta yanke shawarar samar da motocin ne don bunkasa tattalin arzikin mambobin kungiyar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here