Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Ayyana Zaman Makoki Na Kwanaki 3 Don Alhinin Rasuwar Sarkin Zazzau

0
107

Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku don jimamin rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Mai baiwa gwamna Nasiru El-Rufai shawara kan kafafen yada labarai, Muyiwa Adeke, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Adekeye ya ce, ofisoshin gwamnati za su kasance a bude kamar yadda suka saba a ranakun 21 da 22 ga watan Satumba. Amma ranar 23 ga watan za ta kasance ranar hutu don girmama mamacin.

Sanarwar ta ce za ayi kasa da tutoci a ranakun jimamin.

Sarkin dai ya rasu ne a jiya Lahadi yana da shekaru 84.

An binne gawar Basaraken a fadar sa dake Zaria kusa da kabarin sauran Sarakunan masarautar.

Babban Limamin Masarautar Zazzau, Dalhatu Kasimu ne ya jagoranci yin Sallah ga mamacin da misalin karfe 5:35 na yamma, wanda dubban jama’a suka halarta.

Wadanda suka halarci jana’izar sun hada da Gwamna Nasiru El-Rufai, Sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Lawal Abbas, Kakakin Majalisar dokokin jihar, Yusif Zailani da sauran manyan jami’an gwamnagi.

An nada Shehu Idris a matsayin Sarkin Zazzau a ranar 15 ga watan Fabarairu na shekarar 1975, Inda ya mulki Masartautar Zazzau Shekaru 45 kafin rasuwar sa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here