Daliban Kwalejin Fasaha ta Kano Sun Yabawa Shugaban Makarantar Bisa Warware Matsalolin Su

0
251

Tsofaffin Daliban Kwalejin fasaha ta jihar Kano(Kano State Polytechnic), sun yabawa shugaban makarantar, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa bisa kokarin warware matsalar daliban da suka gaza biyan kudin Registration na Spill over wanda ya kai ga an kore su.

A wani taron sada zumunci da kungiyar tsofaffin daliban, yan ajin shekarar 2016 suka shirya sun kuma yi jinjina ga hukumomi da malaman makarantar bisa dafawa da suka yi wajen warware matsalar daliban.

Mubarak Dalhat, shine jagoran kungiyar daliban ya bayyana cewa sun shirya taron ne don nuna farin cikin su bisa sahalewar da hukumomin makarantar suka yi na sake yin duba kan matsalar daliban.

 

“Babban Muhimmin taro shine, akwai daliban da suka samu matsala wacce ta kai ga an kore su, bayan haka mun tattauna da hukumomin makaranta, wadanda suka amince zasu tallafawa daliban.

“Anan muke so mu jinjinawa shugaban wannan makarantar bisa duba kukan dalibai”. Ini jagoran daliban.

Shima Sakataren kungiyar Daliban, Bashir Garba Isah ya bayyana farin cikin sa ga hukumomin makarantar bisa warware matsalar da dalibai ke shiga.

Wasu daga cikin daliban da suka halarci taron sun yabawa, hukumomin makarantar bisa warware matsalar su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here