Zaben Edo: Mun Gamsu da Sakamakon Dake Fitowa a Halin Yanzu -PDP

0
159

Nyesom Wike, Gwamnan jihar Rivers ya ce zai aminta da duk wanda aka bayyana cewa ya samu nasara a zaben jihar Edo.

A jiya Asabar ne dai mazauna jihar Edo suka yi dafi-fi wajen zaben wanda zai jagoranci jihar na tsawon shekara hudu.

Yayin da yake jawabi ga yan jarida a gidan gwamnatin jihar dake Benin, babban birnin jihar, Wike,  wanda shine shugaban kwamitin yakin neman zaben jami’iyyar PDP, ya ce jami’iyyar ta gamsu da sakamakon dake fitowa na zaben da aka yi.

Sannan ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da jami’an tsaro bisa gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.

“A yanzu bani da ikon sanar da sakamakon zabe, amma daga rahotannin da muke samu, ina tunanin muna cikin farin ciki”, cewar Wike.

“Ina son yabawa INEC bisa tabbatar da cewa mutane sun yi zabe a rumfunan zabe.

“Zan kuma yabawa jami’an tsaro bisa tabbatarwar da suka yi ba a samu rikici ba, matukar hakan ya ci gaba, ina fatan an samu nasara.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here