Yanzu-Yanzu: Sarkin Zazzau Ya Rasu

0
527

Bayanan dake shigo mana yanzu-yanzu na bayyana cewa Sarkin Zazzau, Mai Martaba Shehu Idris ya Rasu.

Shehu Idris, Wanda ya shafe shekaru yana kan karagar mulkin masarautar Zazzau ya rasu ne a Abuja.

Ana saran za’ayi jana’izar sa nan gaba kadan da zarar an kawo gawarsa daga Abuja.

Marigayi Shehu Idris ya halarci sallar Jumaar data gabata a birnin zazzau a inda Kammala salar keda wuya rashin lafiya ta kamashi a inda aka wuce neman magani dashi.

Birnin zazzau yayi tsit sakamakon rasuwar sarkin a inda a wasu guraren aka Sanya sauti na karatun qurani.

Zaa kawo gawar mai martaba Sarkin birnin zazzau don masa suttura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here