Obaseki Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Edo Karo na 2

0
185

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar a jihar.

Obaseki ya lashe zabe a karo na biyu bayan samun kuri’u mafiya rinjaye.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da Obaseki na jami’iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara a zaben.

Obaseki ya kayar da babban mai hamayya da shi, Osagie Ize-Iyamu na jami’iyyar APC.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here