Obaseki Na Jami’iyyar PDP Ya Kama Hanyar Lashe Zaben Jihar Edo da Gagarumin Rinjaye

0
177

Gwamnan Godwin Obaseki na jami’iyyar PDP na kara samun nasara bayan ya lashe zaben kananan hukumomi 8 daga cikin 12 da aka bayyana.

Jami’iyyar PDP, kamar yadda aka sanar da sakamakon zabe ta bawa jam’iyyar APC tazarar kuri’u dubu 50.

Jami’an hukumar zabe na INEC ne dai suke bayyana sakamakon zaben daga kananan hukumomi.

A karamar hukumar Esan South-East, Obaseki ya samu kuri’u 10, 565, yayin da Ize-Iyamu ya samu 9, 237. A Esan North-East, Gwamna Obaseki ya samu kuri’a 13, 579 yayin da Ize-Iyamu ya samu kuri’a 6, 559.

A karamar hukumar Esan Central, PDP ta samu Kuri’a 10, 963 yayin da APC ta samu 6, 719. A Igueben, Obaseki ya samu kuri’a 7, 870 yayin da Ize-Iyamu ya samu kuri’a 5, 199.

A Ihunmwode South-South, PDP ta samu kuri’a 10, 022 yayin da APC ta samu 5, 972.

A kananan hukumomi 12 da aka sanar, PDP ta samu kuri’u 202, 574 yayin da APC ta samu Kuri’u 154, 704.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here