Kwankwaso Ya Taya Obaseki Murnar Lashe Zabe

0
281

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya taya gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, Murna bisa nasarar sake lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar jiya Asabar.

A wata sanarwa da mai taimakawa Sanata Kwankwaso kan kafafen yada labarai, Saifullahi Hassan ya fitar, a yau Lahadi, Kwankwaso ya kuma taya al’ummar jihar ta Edo murna tare da jinjina musu bisa zabar jami’iyyar PDP.

Kwankwaso ya kuma bayyana farin cikin sa ga shugabanin kungiyar Kwankwasiyya da na Kungiyoyin yan Arewa bisa goyan bayan da suka bawa jami’iyyar yayin zaben.

A yau ne dai hukumar zabe ta ayyana dan takarar jami’iyyar PDP, Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da gagarumin rinjaye bayan ya doke dan takarar jami’iyyar APC, Ize-Iyamu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here