Zaben Edo: Tambuwal Ya Yabawa Buhari

0
158

Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban gwamnonin jami’iyyar PDP, Aminu Tambuwal ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo,  da su bi dokoki tare da tabbatar da abinda mutanen jihar Edo suka zaba.

Gwamna Tambuwal a tattaunawar da yayi da manema labarai a jihar Sokoto ya ce bayanai daga jihar Edo na bayyana cewa yadda ake gudanar da zaben abin yabawa ne.

Tambuwal ya ce hukumar zabe ta kasa INEC da sauran hukomin gwamnati da suke da ruwa da tsaki a zaben su samar da yanayi mai kyau ga jama’ar Edo wajen yin abinda yake hakkin su ne ba tare da takurawa ba.

Gwamnan ya yabawa shugaban kasa Buhari bisa umarnin da ya bayar ga dukkan jami’an tsaro da su zama basa goyan bayan kowa a zaben.

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Edo da yan siyasa da su tabbata anyi zabe ba tare da rikici ba kuma an bi ka’idojin da aka tsara na zabe.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here