Wani Mai Bayar da hayar gida Ya Kona matar dake haya a Gidan sa Kan Bashin Kudi 11, 000

0
129

Wani mai bada hayar gida ya kunna wuta a dakin daya daga cikin masu hayar gidan sa bisa rike masa bashin Naira Dubu 11.

Rahotanni sun bayyana cewa, wacce abun ya faru akanta mai suna Misis Mary Samuel,ta rasa ran ta,  a ranar Laraba, yayin da wanda ya bata hayar gida, a No 9, Ansa Ewa Street David Okon ya zuba man fetir a dakin da matar ta ke kana ya cinna masa wuta.

Daya daga cikin mazauna gidan hayar mai suna Obongette, ya ce “Matar ta na siyar da kifi, a ranar Laraba ta je ta siyo kifi a Orun na jihar Akwa Ibom , yayin da ta dawo da yamma, mai bayar da haya ya tambaye ta cikon kudin hayar da ake bin ta, sai ta ce ba ta da kudi ya kyale ta, ta siyar da kifin ta yadda za ta hada kudin ta biya.

” Sai dai mai gidan hayar ya fusata da bukatar matar sai ya fara yi mata fada kan kin biyan sa kudin haya, yayin da matar taje wanka, mutumin sai ya zuba fetir a dakin, bayan ta fito daga wanka ta shiga dakin sai mutumin ya cinna mata wuta.

“Matar ta fara kururuwa tare da kokarin tsira da rayuwarta, mutumin ya kulle dakin, yayin da mutane suka zo kubutar da ita sai ya fito da ashana yana korar su tare da yin barazanar kashe duk wanda yayi yunkurin ceton matar dake ci da wuta.”

Obongette ya ce bayan mutuwar matar, makota a yankin sun taru tare da daukar gawar ta zuwa gidan mai bada hayar har sai da yan sanda suka zo suka dauke ta zuwa wajen ajiye gawarwaki.

Gidan dai mahaifin sa ne ya gina kafin rasuwar sa sai dai ya kori dukkan yan uwan sa daga gidan tare da mallake shi”.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magan da yawun rundunar yan sanda ta jihar, Irene Ugbo, ya ce jami’an yan sanda sun kama mutumin yayin da gawar aka kaita wajen ajiye gawarwaki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here