Mataimaki Ga Shugaba Buhari, Zai Angon ce

0
240

Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, ya sanar da ranar 25 ga watan Satumba, a matsayin ranar bikin sa.

Ya bayyana ranar ne a shafin sa na Twitter, in da yace zai Auri Naeemah wacce yar asalin jihar Katsina ce.

“Ranar da aka jima ana jira ta zo! Ni da Naeemah muna farin cikin gayyatar ku zuwa daurin auren mu a ranar 25 ga watan Satumba, a masallacin juma’a na GRA dake jihar Katsina da misalin karfe 2 na rana. Idan baka samu damar halarta ba, ka sanya mu cikin addu’ar ka”, kamar yadda Bashir Ahmad ya wallafa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here