Masu garkuwa da mutane sun sako wani tsohon sojan Amurka a Ekiti

0
141

Bayan kwashe kwanaki hudu a tsare, wadanda suka sace wani tsohon hafsan sojan Amurka kuma dan asalin Ijan Ekiti a Ekiti, Mista Jide Ijadare sun sake shi.

An sace Ijadare da misalin karfe 2.05 na rana a ranar Talata a masana’antar noman dabino tare da daya daga cikin ma’aikatansa.

Wani dan kwangila da ke aiki tare da masana’antar shi ma maharan sun kashe shi.

Wata majiya daga dangin ta shaida wa manema labarai cewa Ijadare ya sake samun ‘yanci ne bayan da ya biya kudin fansar da masu garkuwar suka nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here