Magoya Bayan Jami’iyyar PDP Sun Fara Murna a Jihar Edo

0
434

Gwamnan jihar Edo, Obaseki ya lashe zaben akwatin mazabar sa yayin da ake ci gaba da bayyana sakamakon zabe a rumfunan zabe a jihar.

A akwatin zabe ta 19, mazaba ta 4 dake Karamar hukumar Oredo, Obaseki ya samu kuri’u 184 yayin da dan takarar jami’iyyar APC, Osagie Ize Iyamu, ya samu kuri’u 62.

Tuni dai Rahotanni suka ce, magoya bayan Obaseki sun fara gudanar da murna a sakamakon farko dake fito wanda ke nuna jami’iyyar PDP ta na samun nasara.

Muna tafe da cikakken Bayani nan gaba kadan….

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here