Kwalejin Fasaha ta Ibadan Ta Kori Lakcara Bisa Zargin Yin Lalata da Daliba

0
129

Hukumar Makarantar Kwalejin Fasaha ta Ibadan(TPI) ta soke daukar aikin da tayiwa Kelani Omotosho, a matsayin Lakcara bisa zargin yin lalata da tsohuwar dalibar makaramtar.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da magatakardar makarantar, Misis Modupe Fawale ta fitar yau Asabar a Ibadan.

Hukumar ta ce , Malamin wanda yake daga sashin koyar da ilimin tsara birane, an kore shi ne bisa zargin bata sunan makarantar.

A wasikar kora daga aiki mai kwanan wata 15 ga Satumba, 2020 kuma mai dauke da sa hannun magatakardar makarantar ta ce “zaka iya tunawa cewa ka aikata dabi’un da ba su dace ba tare da yin mummunar alaqa tsakanin ka da tsohuwar daliba.

” Wannan aikin ya bada kunya tare bata sunan wanda ya dauke ka aiki, Kwalejin fasaha ta Ibadan.

“Za kuma ka iya tunawa da martani da gurfanar ka gaban kwamitin bincike.

“Bayan lura na tsanaki kan wannan lamari, majalisar gudanarwa ta same ka da laifi a ayyukan ka da mu’amalar ka wacce ta nuna rashin Da’a.

“Don haka majalisar gudanarwa ta amince a soke daukar aikin da aka yima daga ranar Juma’a 11 ga watan Satumba, 2020.

“Ka mika duk abin da ya zama mallakin makaranta ne a hannun ka ga shugaban sashin da kake”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here