An Kama Wata Mata A Tarauni Dake Jihar Kano Bisa Zargin Kashe Dan Kishiyar ta

0
186

Hukumar dake yaki da fatauci da cin zarafin yara ta kasa a jihar Kano ta kama wata mata yar shekara 29, mai suna Jamila Abubakar, bisa zargin kashe dan kishiyar ta, Mohammed Bashir.

Kwamandan hukumar na jihar Kano, Shehu Umar, ya ce an kama wacce ake zargin ne a ranar Alhamis, bayan dukan da tayiwa yaron dan shekara 7 wanda ya rasa ran sa a kasuwar Tarauni dake cikin Birnin Kano.

Umar ya ce a kwanakin baya hukumar ta gayyaci matar bisa zargin cin zarafin kananan yara bayan kubutar da yaron da ya rasu wanda ta daure shi a daki ba tare da bashi abinci ba.

Kwamandan ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na kasa cewa hukumar ta NAPTIP samar da kayan sawa da magani ga yaron bayan mika shi ga mahaifin sa bayan ma’auratan sun yi rantsuwar baza su sake wulakanta shi ba.

Umar ya ce “Cikin rashin sa’a, yaron an yi masa duka wanda ya jawo ya rasa ran sa. lamarin an mika shi ga hannun yan sanda dun gudanar da cikakken bincike”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here