Zaben Edo: Jami’an Tsaro Sun Killace Gwamnonin Mu -PDP

0
360

Jami’iyyar PDP ta yi kukan cewa jami’an tsaro a Birnin Benin na jihar Edo sun killace gwamnonin ta a yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar a gobe Asabar.

Sanarwar da jami’iyyar ta PDP ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jami’iyyar Kola Ologbondiyan ta ambato shugaban jami’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus yayin taron manema labarai na bayyanawa al’ummar kasa cewa,  jami’an tsaro sun yiwa inda gwamnonin PDP suke kawanya.

Jami’iyyar ta bayyana kaduwa da cewa jami’an tsaro sun kewaye masaukin gwamnonin ne don su matsa musu kuma su ci zarafin su, yayin da gwamnonin APC da suka hada da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Imo Hope Uzodinmma da mataimakin shugaban majilsar dattawa, Ovie Omo-Agege a ka bar su cikin walwala a masaukin su dake gidan tsohon shugaban jami’iyyar APC na kasa Adams Oshiomale.

“A kowanne irin matakai, muna da kwarin gwiwar cewa, gwamnonin mu baza su bari a wulakanta su ba” inji jami’iyyar.

Jami’iyyar ta PDP ta yi Kira ga masu ruwa da tsaki a zaben gwamnan na jihar Edo musamman jami’an tsaro da su yi aiki don ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here