Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta Nemi Afuwar Yan Najeriya Bisa Neman su Cike Form din Bayanan su a Bankuna

0
150

Gwamnatin tarayya ta nemi afuwa bisa neman masu asusu a bankuna da su kara shigar da bayananan su a bankuna.

Rahotanni dai sun bayyana cewa gwamnati ta nemi masu asusu a bankunan kasarnan da kamfanunuwan inshora da su sake cike form din bayanan su.

Umarnin da gwamnatin ta bayar a jiya Alhamis ya zo ne duk da cewa akwai bayanan BVN da na Katin shedar dan kasa da gwamnatin ta ke da shi.

Umarnin na sake cike wani form na daban ya jawo cece-ku-ce a shafukan sadarwa na zamani.

Sai dai a yau Juma’a, Gwamnatin ta nemi afuwa kan lamarin.

a sakon da gwamnatin ta wallafa a shafin ta na Twitter ya ce “Muna neman afuwa bisa kuskuren wallafa bayanin(wanda yanzu an goge shi) wanda ya shafi cike form dkn bayanai”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here