Masu Neman Kujerar Gwamnan jihar Kano a Zaben Shekarar 2023

0
612

Yayin da gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yake da shekaru uku nan gaba don kammala wa’adin mulkin sa, rahotanni sun bayyana cewa an fara shirye-shiryen karkahin kasa don fitar da wanda zai gaji gwamnan.

Duk da lokaci bai yi ba na fitar da yan takara a zaben shekarar 2023 amma yunkurin manyan yan siyasar Kano na nuna cewa Kano za ta zama Cibiyar da siyasa za ta dau zafi a arewacin Najeriya.

A yanzu haka akwai yan siyasar da suka fara nuna sha’awar su ta fitowa takarar kujera mafi tsada a jihar a shekarar 2023 mai zuwa.

Jaridar Leadership ta rawaito cewa wani wanda ya taba zama Kwamishinan kudi a Kano ya bayyana ra’ayin sa kan lamarin, in da ya ce akwai yan takarkari da yawa a yanzu wadanda suka bayyana bukatar su ta gadar Abdullahi Umar Ganduje, wasu acikin jami’iyyar APC wasu a PDP.

Jaridar ta rawaito cewa, Kusa a jami’iyyar ta APC wanda ya nemi a boye sunan sa ya ce wasu daga cikin yan takarar, sun taba tsaya takara yayin da wasu suke son gwada kwanjin su a karo na farko don bunkasa siyasar su.

Ya ce kwananan yan takarar za su fara fadar bukatar su kai tsaye da kuma jami’iyyar da suke muradin ganin mafarkin su ya cika.

Wata majiyar ta daban a ofishin jami’iyyar APC na Kano dake Hotoro, Kwanar Maggi ta fadawa jaridar ta LEADERSHIP cewa yan takara da dama sun bayyana aniyar su ta neman kujerar gwamnan a zaben shekarar 2023.

Ya ce takarar Sanata Barau Jibrin Maliya, tsohon gwamna kuma sanata a yanzu Kabiru Gaya da Alhaji Usman Alhaji, Sakataren gwamnatin jihar ta bayyana a fili.

Haka abun yake a bangaren kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, wanda ake ganin yana fafutuka ta karkashin kasa wajen zama gwamnan jihar Kano kuma yana da goyan bayan shugabannin kananan hukumomi 44 a jihar.

Sannan akwai mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusif Gawuna wanda aka ce ya na samun goyan bayan manyan kungiyoyi a jihar. Kuma ya na tada gudanar da taruka gami da tuntuba don ganin ya cimma burin sa a shekarar 2023.

Haka kuma akwai Abdulkadir Inuwa Waya, wanda ake ganin sabo a fannin siyasa sai dai bukatar takarar sa tana tafiya a karkshin kasa, bukatar sa shine zama gwamman jihar Kano a zaben shekarar 2023.

Binciken jaridar LEADERSHIP ya gano cewa Abdulqadir Waya yana da kudi wanda zai yi amfani da su don ganin cikar burin sa.

Shima Salihu Sagir Takai, wanda ake ganin dan takara ne da ya yi sanyi, ya bar jami’iyyar PRP zuwa APC a kwanakin nan bisa bukatar magoya bayan sa Wadanda suka bukaci chanza jami’iyya don sake yin takara a zaben shekarar 2023.

Sannan akwai yuwuwar Takai zai sake yin kawance da tsohon maigidan sa, Sanata Ibrahim Shekarau, don sake neman takarar kujerar gwamnan Kano karo na 4 ba tare da yin nasara ba a baya.

Sai dai ana ganin da wahala Takai ya gamsar da yan gidan Shekarau bisa zargin kalaman da aka ce yayi ga maigidan su yayin da shekaran ya bar jami’iyyar PDP a zaben shekarar 2019.

A dai jami’iyyar APC din wasu na ganin Ahmad Idris, babban Akanta Janar na Kasa na daga cikin yan gaba-gaba wajen neman kujerar gwamnan jihar Kano wanda kuma yake da goyan bayan gwammatin tarayya kasancewar sa kusa a gwamnatin shugaban kasa Buhari.

A bangaren jami’iyyar PDP kuma wani jigo a jami’iyyar ya fadawa Jaridar LEADERSHIP cewa jami’iyyar na shirin sake bawa Abba Kabir Yusuf Dama a shekarar 2023, mutumin da ya nuna kwazo wajen karawa da gwamna Ganduje a zaben 2019.

Sannan ya ce PDP wacce ita ce babbar jami’iyyar adawa a jihar za ta bawa Abba Gida-Gida dama ta biyu saboda alaqar sa da tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso.

Yanzu dai za’a iya cewa lokaci ne kadai zai bayyana wanda zai kasance a matsayin gwamnan jihar Kano a zaben shekarar 2023.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here