Gwamnatin Najeriya ta yi Martani ga Kasashen Amurka da Burtaniya

0
170

Gwamnatin Najeriya ta nemi Kasar Amurka da Burtaniya da su dena raina Najeriya da Yan Najeriya.

Gwamnatin na mayar da martani ne ga sanarwar da kasar Amurka da Burtaniya suka yi kan zaben gwamnan da za’ayi a jihohin Edo da Ondo.

A sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen waje na Najeriya, Ferdinand Nwonye ya fitar, ta bayyana damuwa bisa kan yadda kasar Amurka ta sanya takunkumin izinin shiga kasar kan wasu yan siyasar Najeriya bisa zargin suna da hannun wajen tayar da rikici yayin zaben gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa.

Sanarwar ta ce “za’a iya daukar sa a matsayin rainin wayo ga kasar Najeriya a ce wata kasa daga waje ta zauna ta yanke hukunci kan halin yan Najeriya ta kuma sanya takunkumi a gare su.

” Gwamnatin tarayya da shugaban kasa sun himmatu wajen samar da kayan aiki, kudi, da tsaro don taimakawa wajen gudanar da zabe.

“Yayin da muke yabawa da tallafi da kwarin gwiwar da kawayen mu suke bamu kamar, tarayyar Turai, muna kira ga kawayen mu irin su Kasar Burtaniya da Amurka da su aiki tare da hukumomin mu wajen ba su bayanan da suke da cikakkiyar sheda kan abin da aka yi ba dai-dai ba don bawa dokokin kasar mu dama su yi aikin su”.

Gwamnatin kasar Amurka dai ta kuduri aniyar daukar mataki kan dukkan wanda ya haifar da rikici yayin zaben gwamnan jihar Edo da Ondo.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here