Zaben Edo: Yan Najeriya Sun Caccaki Bola Tinubu

0
140

Wasu yan Najeriya sun caccaki jagoran jami’iyyar APC, Bola Tinubu, biyo bayan sukar da ya yiwa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, a wani faifan bidiyo da yayi yawo a kafafen sadarwa.

Tinubu dai a ranar Talata ya bukaci masu kada kuri’a a jihar Edo da su kauracewa zaben Obaseki, wanda ke neman a sake zaben sa a karo na biyu.

Yayin da yake jawabi a wani Bidiyo da aka haska shi a gidan talabijin na TVC, Tinubu ya ce yakamata mutane su yi waje da Obaseki a zaben ranar Asabar.

Obaseki dai shine dan takarar jami’iyyar PDP a zaben da za’a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.

Tinubu ya soki Obaseki da kasancewa dan kama karya a jihar Edo.

Ya ce, “Ina son na yi kira a gare ku, kada ku zabi Godwin Obaseki a zaben nan mai zuwa. Na sha wahala ni da wasu da dama kan wannan lokaci na dimukuradiya wacce a yau muke morarta a kasarnan.

“Sannan, Godwin Obaseki bai yi fafutuka ko daya ba wajen tabbatuwar dimukuradiyya a kasarnan.

“Don haka ba zai fahimci kima da irin wahalar da wadanda suka yi fafutukar kafa dimukuradiyya suka yi ba.

” Bai chan-chanci samun kuri’a ko daya ba. Kada ku zabe shi. Ina kira a gare ku.

Sai dai wasu yan Najeriya na ganin sukar da Bola Tinubu ya yi ga Obaseki a bar Allah wadai ce.

In da suka yi bayanin cewa jagoran APC din bashi da alhakin fadawa mutane wanda za su zaba a yayin zabe a kasarnan.

Wani mai suna Prince Zephaniah, ya bayyana Tinubu a matsayin wanda ba dan dimukuradiyya ba bisa sukat Obaseki a faifan Bidiyo.
Inda ya ce “Baza ka kara yaudarar wannan al’umma ba”.

Shima Akorede Oladipupo ya ce Tinubu akwai bukatar yasan cewa yan Najerita fa wayayyu ne a yanzu.

“Ni bana goyan bayan kowacce jami’iyya saboda duk kanwar ja ce, amma ta yaya wanda ke kiran kan su dan dimukuradiyya zai nemi mutane kar su zabi wan, gaskiya ba dan dimukuradiyya ba ne” inji shi.

Akinyemi Opeyemi, shima ya bayyana ra’ayin sa da cewa
“Shi(Tinubu) bai damu da matsalar tsaro da matsin da ake ciki ba a kasarnan.” Inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here