Talauci ne Babban Makamin Najeriya Wajen Yaki da Annobar COVID-19 – Dr. Sani Aliyu

0
128

Majalisar dattawa a jiya Talata ta bibiyi yadda kasarnan ke yaki da annobar COVID-19 in da majalisar ta bayyana cewa tsarin kasashen turai da kwamitin kar ta kwana na fadar shugaban kasa kan yaki da cutar ke bi na kashe tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai, Babban Jami’in kwamitin, Dr. Sani Aliyu, ya ce Talauci shine babban makamin da ake a amfani da shi a Najeriya wajen yaki da annobar.

Dukkan bangarorin sun yi magana a taron tattaunawa tsakanin hadin gwiwar kwamitin majalisar dattijai kan fannin lafiya da zirga-zirgar jiragen sama, mambobin kwamitin kar ta kwana da sauran masu ruwa da tsaki a fannin lafiya.

Yayin da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin majalisar dattijai kan fannin zirga-zirgar jiragen sama, Sanata Smart Adeyemi, ya bayyana cewa cutar COVID-19 gaskiya ce, amma ba ta yi kamari a Najeriya da sauran kasashen Africa ba.

Adeyemi ya ce bisa abin da ake gani a zahirance, ba dai-dai bane masu ruwa da tsaki a kasarnan su hadiyi gatari a baki tare da daukar matakan da kasashen turai, Amurka da China ke dauka”.

Ya ce “Akwai abin da muke da shi mu yan Afrika wanda ba su da shi a kasashen turai da Amurka, wanda ya sa cutar COVID-19 ba ta yi muni anan ba kamar yadda tayi a chan.

“Bisa abin da ya bayyana a haka, matakan da za su matsawa rayuwar yan Najeriya dole ne a kauce mu su, don kar a kashe tattalin arzikin kasa”.

A yayin da take nata jawabin, Sanata Biodun Olujimi ta tambayi babban jami’in kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19, dalilan samun nasarar yaki da cutar a Najeriya.

Dr. Sani Aliyu ya mayar da martani in da ya ce akwai talauci cikin dalilan samun nasarar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here