Saidawa: Kauyen da Ba su Taba Ganin Service din Waya ba A Kano

0
271

Mazauna garin Saidawa dake karamar hukumar Danbatta a jihar Kano, sun koka kan cewa garin bai taba samun damar yin kiran waya ko shiga kafar sadarwa ta Internet ba(Service).

Mazauna garin sun sheda cewa basa samun Service har sai sun hau wani babban dutse ko bishiya, wanda hakan ya jawo jama’a da dama suka ji raunika.

Wani mutum a garin da ya nemi a boye sunan sa ya ce basa samun damar shiga kafafen sadarwa don cike form din shirye-shiryen daukar aiki, ko jarrabawa da gwammati take yi.

“Akwai mutumin da ya fado ya karye yayin da ya hau saman bishiya don samun damar yin kiran waya, tunda muke a garin nan bamu taba samun service ba”, cewar mutumin.

Shima wani mazaunin garin ya ce lamarin yana shafar harkar tsaro a garin ta yadda ba su damar yin kiran waya ga jami’an tsaro, idan wani lamari ya faru.

“Ba mu taba kiran jami’an tsaro a waya ba, ko jami’an kashe gobara, saboda babu damar yin kiran, muna tsoron ace wata matsala ta samu a garin nan, saboda ba mu san yadda za mu yi mu kira waya a kawo mana agajin gaggawa ba”.

Shima wani matashi a garin ya ce matsalar rashin service na waya yana shafar kasuwanci da sada zumunci a garin.

” Babu damar ka kira waya daga nan zuwa birni, balle kayi kasuwanci ko ka gaida yan’uwan ka balle ka hau kafar sadarwa ta Internet don gaisawa da abokan arziki”.

Shima wani manomi a garin yace basa samun labarin tallafin noma da gwamnati ta ke bayarwa saboda matsalar rashin service

“Mu dai bamu san ma ta ina zamu nemi tallafin noma ba, bamu da seevice a garin nan, kiran waya ma sai mun hau saman bishiya”.

Sannan mazauna garin sun ce abu ne mai matukar wahala ga dan garin ya samu damar shiga manyan makarantu, saboda babu damar shiga shafukan neman gurbin karatu.

Sai dai wata Majiya ta shaidawa Jaridar PRIME TIME NEWS cewa kamfanin MTN ya kuduri aniyar zuwa garin domin samar da service.

Jaridar PRIME TIME NEWS za ta cigaba da bibiyar hukumomin da abun ya shafa don ganin an samar da service a kauyen na Saidawa.

Wasu na ganin dai ana barin kauyuka da dama a fannin samar da abubuwan ci gaba, kamar makarantu, gine-gine da sauran su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here