Gwamnatin Jihar Kano ta Kashe Naira Miliyan 159 Wajen Gyaran Makarantun Kwana na Almajirai

0
119

Gwamnatin jihar Kano ta kashe kudi Naira Miliyan 159 wajen gyaran makarantun kwana na Almajirai(Tsangaya) a jihar.

Alhaji Sanusi Kiru, kwamishinan ilimi na jihar Kano ne ya fadi hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Aliyu Yusif ya fitar.

Kwamshinan, wanda ya duba yadda gyaran makarantun ke gudana, ya ce makarantun suna kananan hukumomin Madobi, Bunkure da Bagwai dake Jihar.

“Gyaran makarantun kwanan ya fara ne tun bayan ziyarar da gwamna Abdullahi Ganduje ya kai yankunan.

“Aikin zai hada da samar da wutar lantarki, gina masallatai, rijiyar burtsatsai da sauran abubuwa,” inji shi.

Ya ce hakan na cikin himmatuwa da kokarin shugabanci na gari, gwamnati za ta cigaba yin hakan don tabbatar da inganta tsarin ilimin almajiranci.

“Kano za ta ci gaba da zama zakara wajen bunkasa tsarin ilimin Almajiranci a kasarnan”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here